Aljannu Bilyan 3 Ne Suka Karɓi Ɗaríkar Tíjjaniyya A Bana – Cewar Sheíkh Ɗahiru Bauchi…

Advertisements

Aljannu Bilyan 3 Ne Suka Karɓi Ɗaríkar Tíjjaniyya A Bana – Cewar Sheíkh Ɗahiru Bauchi

AUREN KIFI DA TSUNTSU: HUKUNCIN AL-KAFA’AH A AURE.

Daga Abdullahi Ibrahim Mahuta.

Advertisements

Watau ba soyayya ce aka hana a tsakanin Kifi da tsuntsu ba, amman dai kafin a ƙulla auren, ya kamata a gano matsalar inda za a zauna, domin rayuwar yau da gobe, la’akari da cewa shi dai Kifi ba ya iya rayuwa a bisa icce. Hakanan shi ma tsuntsu ba ya iya rayuwa a cikin ruwa…

A lokacin da na ke zaune a Maiduguri, shekara kamar 14 kenan da su ka wuce, ina da wani aboki da ke neman wata yarinya da aure. Wannan yarinyar kuma ta kasance ɗiyar ɗaya daga cikin manya manyan attajirai na wannan gari. Shi kuma aboki na ana iya sanya shi a matsayin middle-class. Shi ba talaka ba kuma shi ba mai kudi ba.

Advertisements

Dukkannin alamu sun tabbatar da cewa yarinyar nan ta na son aboki na da gaske. Kuma ta na da niyyar auren shi. To Amman shi kuma a kullun su ka hadu da ita, ya kan dawo da fargaba. Kullun ya je wurin ta, kara tsorata shi ta ke yi.

“Wai kai mallam ni na ga kullun ka dawo daga wurin yarinyar nan, maimakon in gan ka cikin annashuwa, sai in gan ka sukuku, duk kamar an zare ma ka lakka. Wai me ke faruwa ne.” Wata rana na tambaye shi.

Aboki na ya amsa ma ni da cewa “Abdullahi, ni fa a’lamarin yarinyar nan ya na ba ni tsoro. Kullun ba ta da wata hira daga labarin lokacin da ta raka wata yayar ta, Ingila, sai na zuwan su Dubai da wata auntyn ta. Ko kuma na zuwan su America ko Saudiyya. Ta dan rinka jefo labarin Abuja ma inda zan iya sa baki, ba ta yi. Yau ma labarin wata yar’uwar su ta ba ni, wadda aka aiko da private jet ya kwashi ‘yan zuwa suna. Sannan kullun mu ka hadu da ita, ko dai za ta kai ɗin ki, ko kuma ta amso din ki. Kuma wallahi duk irin manya manyan atamfofin nan ne da leshi ma su tsada. Anya kuwa ban ‘dauko Kano ba gammo ba’”

Wata rana na raka shi zance, sai ta ke ba mu labarin wata yar’uwar su da su ka rabu da mijin ta. Ta na ta zagin mijin ta na nuna tsananin rashin mutuncin shi. Sai na ce mata ni kam zan so jin irin rashin mutuncin shi. Sai ta ce ma ni to bari in ba ka misali:

Advertisements

“Wata rana su ka shirya za su je yawon shakatawa Dubai. Irin family outing din nan. To dama diyar su daya about one year. Sai matar ta ce a tafi da nany mai kula da baby. Shi kuma mijin ya ce gaskiya ba za a tafi da nany ba. So ya ke su tafi su uku kawai. Daga shi sai matar shi sai kuma babyn su. Saboda rashin mutunci irin na shi, hakanan ya bar ta ta yi ta wahala da baby a Dubai ita kadai” Mu ka hada ido da aboki na na ce “eh lallai bai kyauta ba kam”…lolsss

Bayan mun dawo gida ya ce ma ni to ka ga fa irin abinda na ke gaya ma ka. Na ce eh lallai kam na fahimci inda matsalar ta ke. Na ce ma shi wannan shine ake ce ma soyayyar Kifi da tsuntsu. Ya ce kamar yaya? Na ce ma shi ka san shi so a zuci ya ke. Ita kuma zuciya kowa ta gadama sai ta so. Ita kuma rayuwar aure rayuwa ce ta zahiri; rayuwa ce ta ƙeƙe da ƙeƙe ba ta zuci ba. Saboda haka idan Kifi da tsuntsu su ka ji su na son junan su, to babu laifi. Amman wace irin rayuwar za ayi? Kuma a ina za ayi ta?

Leave a Comment