Zargin Da Akemin Na Shigowa Film Da Aure Karya Ne – Cewar Humaira Amaryar Tiktok

Advertisements

Jaruma Aisha Usman da aka fi sani da Humaira matar Sule a shirin nan mai nisan zango na ‘Zaman Aure, Amaryar TikTok’ ta ce ba ita ce jarumar da ake zargin ta shigo film da aurenta ba.

Humaira amaryar Tiktok ta bayyana hakan ne a wata ziyara da ta kaiwa Freedom Radio a ranar Laraba 11 ga Janairu.

Ta ce, ita da mahaifiyarta sun sha gursheƙen kuka sakamakon sakonnin da take samu bayan da aka yaɗa rahoton cewa, ita ce ta bar mijinta ta shigo film.

Advertisements

Ga ƙarin bayanin da ta yiwa wakilin Freedom Radio Abdurrahman Hamisu Namadina. 👇👇👇

Leave a Comment