Yanzu-Yanzu: An Hallaka Wata Mata Mai Ciki Da Ƙanwarta A Kano

Advertisements

Yanzu-Yanzu: An Hallaka Wata Mata Mai Ciki Da Ƙanwarta A KanoRahotonnin da Freedom Radio ke samu yanzu haka na cewa an samu gawar wata mata mai suna Rabi da ƙanwarta ƙarama da take riƙo a gidanta da ke unguwar Rijiyar Zaki Fadama a Kano.Mijin matar mai suna Sagir Mai magani ne ya yi arba da gawarwarkin cikin jini a wannan daren lokacin da ya dawo gida.Yanzu haka tuni ƴan sandan Rijiyar Zaki suka ɗauke gawarwakin mamatan domin ci gaba da bincike.

Leave a Comment