Tsohon mijin jaruma momee Gombe ya bayyana dalilin da yasa zai kara auren wata jaruma

Advertisements

Tsohon mijin jaruma momee Gombe ya bayyana dalilin da yasa zai kara auren wata jaruma

Wasu suna fada cewa shi wannan mutumin bashi da wani aiki kullum sai dai yana bibiyar Jaruman kannywood yana aura baya wasu kuma suna yi musu wani kallo na daban amma daman bahaushe yana cewa abincin wani gubar wani dan haka shima yake ganin babu wasu mata wanda suka dace dashi illa wa’yannan jaruman yan Film

A baya dai shine wanda ya auri mome gombe wanda kuma Allah baiyi zaman nasu bame dadewa bane wanda a halin yanzu sun rabu kuma saiga wata sabuwar sanarwa wacce zai auri wata daga cikin jaruman kannywood

Advertisements

A zantawar da akayi dashi yace babu wata matsala da suka samu da tsohuwar matar tasa kawua dai kaddara ce wacce bata wuce kowa ya sameta ba a zamantakewar zaman aure itace ta rabasu kuma basu da da ko ya

Yanzu kuma ba watace wacce zai aura ba illa Minal Ahmad wacce kukafi sani da Nana ta cikin shiri mai nisan zango wato izzzar so itace wacce zata maye masa gurbin jarima momee Gombe a zaman aure

Advertisements

Mudai fatanmu shine Allah ya basu zaman lafiya ya kuma sanya alheri acikin wannan zaman nasu na aure ta kuma basu zuri’a dayyiba amin

Leave a Comment