Yadda Aka Kama Saurayin Da Yayi Fice Wajen Lalata Da Matan Mutane

Advertisements

Wani mutum da ke yaudarar mata masu neman aiki yana yin lalata da su ya fada a komar jami’an tsaro.


Yan sanda sun cafke mutumin mai shekara 50 ne bayan ya rika yaudarar mata masu neman aikin gwamnati yana musu alkawarin tare da kai su otel yana yin lalata da su.

Yan sanda a Bayelsa sun gano dan damfarar yakan yi sojan gona ne a matsayin jami’in gidan gwamnatin jihar, inda yake yaudarar mata tare da yi musu alkawarin aiki.

Advertisements

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya ce asirin dan damfarar ya cika ne bayan daya daga cikin ’yan matan ta kai kara, aka cafke shi a unguwar Opolo da ke garin Yenagoa.

Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike gabanin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Advertisements

Leave a Comment