Yadda Amarya Ta Fita Da Gudu Bayan An Ɗaura Aure Lokacin Da Abokin Ango Ya Rufata Da Duka

Advertisements

Bayan ta gano angon dan giya ne mai dukan mata, wata amarya wacce bata daukar raini ta tsere ta bar angonta bayan awanni 10 dadaurin aurensu.

Hakan ya biyo bayan yadda ya yi tatil da giya ya hau dukanta.

Wani abokin aikinta cike da takaici ya wallafa labarin yadda lamarin ya auku a shafinsa na Twitter Kamar yadda abokin aikin amaryar mai amfani da suna bright r ya wallafa, sai da ango yasha giya yayi tatil kafin su isa otal din
da za ayi shagalin bikin.

Advertisements

Su na zaune a otal din sai wani sabani ya shiga tsakaninsu daga nan angon ya kasa hakura ya fara dukan amaryar tasa.


Ga Yadda wallafar ta ke”Akwai wata abokiyar aikina da ta yi aure amma ta bar mijin bayan an daura musu aureda awanni 10.

Advertisements

“Alamu sun nuna yadda ya yi tatil da giya sannan ya isa otal din da suka kama don shagalin bikin daga nan ya hau dukanta saboda wani dalili.

“Take anan ta dauki kayanta ta tsere,
hakanan fa ta wuce,” kamar yadda brightr
ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, 29 ga watan Disamban 2021.

Tirkashi Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari, Kada Ku Manta Ku Danna Alamr Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-sbiryenmu Akoda Yaushe.

Leave a Comment